Isa ga babban shafi
Japan

Firaministan Japan Shinzo Abe zai zarce da iko har shekara ta 2021.

Wata sabuwar dokar da jam'iyar dake mulki a kasar Japan ta fito da shi ya baiwa Firaministan kasar Shinzo Abe ikon zarcewa da mulki har shekara ta 2021.

SFiraministan Japan Shinzo Abe tare da Shugaban Amurka Donald Trump
SFiraministan Japan Shinzo Abe tare da Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Jim Bourg
Talla

A yau lahadi jam'iyar ta LDP ta amince da sabon dokan a babban taron jiga-jigan Jamiyar da aka yi.

Karkashin tsohon tsarin Firaministan zai sauka a watan Satumba na badi koda jam'iyar ke mulki.

Karkashin sabon tsarin Firaministan na iya sake tsayawa takara a zaben badi da za'ayi.

Shinzo Abe mai shekaru 62 ya dana kujeran Firaminstan na kusan shekara daya amma ya sauka a shekara ta 2007 saboda rashin nasarar zabe a Babbar majalisar kasar.

A shekara ta 2012 ne kuma ya sake samun nasarar hawa kujeran Firaminista, bayan zama a bangaren adawa na shekaru uku.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.