Isa ga babban shafi
Brazil

Aljannu sun kori Shugaban Brazil daga Fadar Gwamnati

Shugaban Kasar Brazil Michel Temer ya ce aljannu sun kori shi daga fadar gwamnati da ake kira Alvorada Palace da ke Brazilia, kuma yanzu haka ya koma zama a gidan mataimakin shugaban kasa.

Shugaban kasar Brazil Michel Temer
Shugaban kasar Brazil Michel Temer REUTERS/Adriano Machado
Talla

Temer mai shekaru 76 ya ce shi da matar sa Marcela mai shekaru 33 kullum sai suyi ta jin wasu kararaki da basu saba ba wanda ke hana su bacci, tun bayan komawa fadar shugaban kasar.

Shugaban wanda ya yiwa Dilma Rousseff mataimaki kafin tsige ta da Majalisa ta yi, ya ce ya koma gidan mataimakin shugaban kasa da ya saba da shi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.