rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Syria Iraqi ISIL Al Qaeda

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shekaru shida da fara boren al'umma a kasar Syria

media
Yanayin yaki a Syria REUTERS/Alaa Al-Faqir

Shekaru shida cur da barkewar boren al’umma da ke nuna fushi dangane da yadda shugaban Bashar Assad ke tafiyar da mulkin kasar Syria, boren da daga bisani ya rikide zuwa yakin basasa.


Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana rikicin na Syria a matsayin mafi muni tun bayan kammala yakin duniya na biyu, inda aka samu asarar rayukan mutane sama da dubu 320, yayin da wasu milyoyi suka gudu suka bar gidajensu.

Wani rahoton bincike da masana suka gudanar, na nuni da cewa a tsawon wadannan shekaru 6, an kashe ma’aikatan jinkai da dama, yayin da aka kashe jami’an kiwon lafiya da ke aikin taimaka wa jama’ar da yakin ya rutsa da su sama da 800.