Isa ga babban shafi
MDD

Mata da 'Yan gudun hijira na fuskantar danniya-MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an samu ci gaba sosai ta fannin kare hakkin bil’adama a fannoni daban daban cikin shekaru 25 da suka gabata. Amma har yanzu akwai wani rukuni na jama’a da ke fuskantar danniya da kuma koma-baya.

'Yan gudun hijirar rikicin Syria da Iraqi na kwarara kasashen Turai
'Yan gudun hijirar rikicin Syria da Iraqi na kwarara kasashen Turai PHILIPPE HUGUEN / AFP
Talla

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tsirarun kabilu, ‘yan gudun hijira, ‘yan ci-rani da kuma Mata ba su amfana da ci gaba da aka sama a shekarun ba.

Yara na zuwa makaranta fiye da shekarun baya, sannan kuma wani adadi na mutane masu yawa na amfana da sauran bangarori na more rayuwa da gwamnati ke samarwa, kamar dai yadda rahoton hukumar samar da ci gaba ta Majalisar Dinkin Duniya UNDP ya bayyana a birnin Stockholm.

Duk da cewa an samu karuwar mutane sama da milyan dubu biyu tsakanin shekarar 1990 zuwa 2015 a duniya, amma rabin wadannan mutane na rayuwa ne a cikin talauci  a cewar rahoton.

Sai dai duk da haka, daya daga cikin mutane uku sun fuskanci matsalar karancin abinci mai gina jiki, yayin da wasu dubu 18 ke mutuwa a kowace rana sakamakon kamuwa da cututukan da ke da nasaba da shakar gurbatacciyar iska a sassan duniya, kuma yawanci mata ne suka fi mutuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.