Isra'ila-MDD
Isra'ila ta ki mutunta kudirin MDD a Falasdinu
Isra’ila ta yi watsi da kudirin Majalisar Dinkin Duniya da ya haramta ma ta ci gaba da gine-gine a yankin al’ummar Falasdinawa, kamar yadda Jakadan Majalisar a yankin gabas ta Tsakiya Nickolay Mladenov ya sanar.
Wallafawa ranar:
Talla
Mladenov ya ce, duk da dai Kwamitin Sulhun ya gabatar da kudirin dakatar da gine-ginen a ranar 23 ga watan Disamban bara, babu wasu matakai da aka dauka.
A cikin watan Janairun daya gabata ne gwamnatin Isra’ila ta sanar da fadada gine-ginenta fiye da dubu 6 a yankin Yamma ga Kogin Jordan da kuma gabashin birnin Kudus da ta mamaye.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu