rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Donald Trump Barack Obama Lafiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump ya gamu da cikas a siyasar Amurka

media
Shugaban Amurka Donald Trump ya samu gagarumin koma baya a fagen siyasar kasar REUTERS/Carlos Barria

Shugaban Amurka Donald Trump ya samu gagarumin koma baya a fagen siyasar kasar bayan Majalisar Wakilai ta janye kudirinsa na samar da inshorar lafiya da za ta maye gurbin Obamacare da tsohon shugaban kasar Barack Obama ya kirkiro.


Mr. Trump dai ya umarci shugaban Majalisar Wakilan kuma jigo a Jam’iyyar Republican Paul Ryan, da ya janye kudirin bayan ya gaza samun karbuwa a gaban Majalisar.

Sai dai a wani martani da ya mayar, Mr. Trump ya yi hasashen cewa shirin Obamacare ba zai yi karko kuma ya zargi ‘yan Jam’iyyar adawa ta Democrat da rusa kudirinsa na samar da sabon shirin kiwon lafiya a Amurka.

Soke shirin Obamacare na cikin muhimman batutuwan da shugaba Trump ya yi alkawari a lokacin yakin neman zabensa.

Kimanin mutane miliyan 20 ne da a can bayan ba su da wani inshorar lafiya ke cin gajiyar Obamacare.