Isa ga babban shafi
MDD

Nukiliya: Amurka ta jagoranci kauracewa zauren MDD

Kasashen Amurka da Birtaniya da Faransa jagoranci kauracewa zauren Majalisar Dinkin Duniya a lokacin da ake tattauna kan yadda za a haramta amfani da makamin nukiliya a duniya.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley REUTERS/Mike Segar
Talla

Kimanin Kasashen duniya 40 da suka hada da Amurka da Birtaniya da Faransa suka kaurace wa zaman cim ma yarjejeniyar haramta amfani da makamin Nukiliya da aka fara gudanarwa a jiya Litinin a zauren Majalisar Dinkin Duniya.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Nikki Haley ta ce, wadannan kasashen da suka kaurace sun mayar da hankulansu ne kan yarjejeniyar takaita yaduwar Nukiliya da ta fara aiki gadan-gadan tun shakarar 1970, a maimakon sabuwar yarjejeniyar haramta makamin baki daya a duniya.

Haley ta kuma jefa tambaya, tana cewa shin akwai wanda ya yi amannar cewa, Koriya ta Arewa za ta amince da haramcin Nukiliyar?

A nashi bangaren, jakadan Birtaniya a Majalisar Mathew Rycroft ya ce , kasarsa ba za ta halarci tattaunawar haramcin ba saboda ba su gamsu cewa, hakan zai kai ga cim ma matsayar kawar da makamin ba a duniya.

Mataimakin Jakadan Faransa Alexis Lamek ya ce matakan tsaro da aka kaddamar ba su kai a dogara da su ba wajen cim ma yarjejeniyar haramta Nukilyar a duniya.

A cikin watan Disamban da ya gabata ne, babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya gabatar da kudirin samar da yarjejeniyar haramta Nukiliya, matakin da kasashe 113 suka goyi baya, yayin da 35 suka nuna adawa da shi, inda kuma kasashe 13 suka kaurace wa zaman.

A makon jiya ne Fadar White House ta bayyana cewa, gwamnatin Donald Trump na nazari dangane da yiwuwar tabbatar da muradin duniya na haramta makamin na Nukiliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.