Isa ga babban shafi
UNICEF

Mutane miliyan 27 a kasashe 4 basa samun ruwan sha mai tsafta - UNICEF

Hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF, ta ce akalla mutane miliyan 27 daga kasashen Najeriya, Somalia, Sudan ta kudu da kuma Yemen ke fama da karancin ruwan sha mai tsafta, wanda ke barazana ga rayukan dubban yara da ke fama da karancin abinci mai gina jiki.

Wasu kananan yara daga Somalia a sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab da kan iyakar Somalia da Kenya.
Wasu kananan yara daga Somalia a sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab da kan iyakar Somalia da Kenya. REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Miliyoyan ‘yan gudun hijira ne ke fuskantar barazanar yunwa sakamakon rikice rikicen da ake a kasashen.

UNICEF ta ce yawan mutanen da ke fuskantar wannan hadarin ya zarta yawan al’ummar Romania da Florida.

Zalika hukumar ta yi hasashen cewa, tsakanin watanni shida mutanen na iya mutuwa saboda yunwa a kasashen guda hudu.

Kari kan haka, UNICEF ta yi gargadin yiyuwar barkewar annobar amai da gudawa a kasashen hudu, wato Najeriya, Somalia, Sudan ta Kudu, da Yemen sakamakon rashin ruwa mai tsabta da rashin muhalli mai kyau da kuma karancin abinci mai gina jiki ga yara da ke rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijira.

A Najeriya UNICEF ta ce ‘yan gudun hijirar rikicin Boko Haram kusan miliyan 4 ne ke rayuwa cikin matsalar rashin ruwa mai tsabta, bayan lalata kusan kashi 75 na hanyoyin samar da ruwan

Mutanen Yemen da sudan ta kudu da Somalia sun fi fuskanatar matsalar ruwan a cewar UNICEF.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.