rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ecuador

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dan takaran zabe a Ecuador ya yi zargin tafka magudi

media
Lenín Moreno, Dan takara da ya lashe zaben kasar Ecuador Foto: AFP

Dan takaran zaben shugaban kasar Ecuador Guillermo Lasso ya yi zargin tafka magudi a zaben shugaban kasar zagaye na biyu da aka yi, inda ya sha alwashin kalubalantar sakamakon da ya baiwa Lenin Moreno nasara.


Hukumar zaben kasar ta bayyana Moreno, dan takarar shugaban kasar mai barin gado, Rafael Correa, a matsayin wanda ya samu sama da kashi 51, yayin da Lasso ya samu sama da kashi 48.

Lasso ya bayyana cewar za su kare kuri’ar jama’ar kasar dan tabbatar da cewar ba a tauye musu hakki ba.