Isa ga babban shafi
Faransa

Gobara ta cinye sansanin 'yan gudun hijira a Faransa

Wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke arewacin Faransa ya kone kurmus bayan tashin wata gobara sakamakon barkewar rikici tsakanin ‘yan gudun hijirar Afghanistan da kuma Kurdawa na Iraqi da ke samun mafaka a cikinsa.

Gobarar ta tashi ne a cikin daren da ya gabata
Gobarar ta tashi ne a cikin daren da ya gabata REUTERS
Talla

Akalla mutane 10 sun samu rauni sakamakon gobarar wadda ta tashi a sansanin Grande-Synthe da ke daukan mutane dubu 1 da 500, kuma Kungiyar Likitoci ta Doctors Without Borders ce ta gina sansanin kafin ta bude shi a bara.

A watan jiya ne, hukumomin kasar suka ce za a rufe sansanin saboda tashe-tashen hankula da ake samu tsakanin mazauna cikinsa.

Rahotanni na cewa, gobarar ba ta bar komai ba a sansanin illa tarin toakar kayayyakin da ta cinye.

A cikin watan Oktoban da ya gabata ne yawan mutanen da ke samun mafaka a sansanin ya karu bayan rufe sansanin dajin Calais da ke da tazarar kilomita 40 tsakaninsa da Grande-Synthe.

Tuni dai aka kwashe ‘yan gudun hijirar don sauya mu su matsugunai na gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.