Isa ga babban shafi
DRC-Belguim

Congo ta yanke huldar soji da Belgium

Jamhuriyar Demokradiyar Congo ta dakatar da huldar soji da ke tsakaninta da Belgium da ta yi ma ta mulkin mallaka, bayan ta caccaki shugaba Joseph Kabila game da nadin Firaministan da ‘yan adawa ba su amince da shi ba.

Shugaba DR Congo Joseph Kabila.
Shugaba DR Congo Joseph Kabila. REUTERS/Kenny Katombe
Talla

‘Yan adawar kasar na kallon nadin Bruno Tshibala a matsayin abin da ya saba wa yarjejeniyar da suka cimma da bangaren gwamnati da zimmar magance rikicin siyasar kasar.

Ma’aikatar tsaron Belgium ta shaida wa kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, Congo ta umarci ofishin sojinta da ke Kinshasa da ya dakatar da duk wata huldar soji tsakanin kasashen biyu.

Rikicin siyasar kasar ya tsananta tun bayan da shugaba Joseph Kabila ya ki sauka daga kujerar mulki duk da karewar wa’adinsa a cikin watan Disamban bara, abin da ya janyo ma sa caccaka daga kasashen duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.