Isa ga babban shafi
Turkiya

Yan adawa sun yi watsi da sakamakon zaben Turkiya

Jam’iyyun adawa na Turkiyya sun bukaci a soke sakamakon zaben raba gardamar da al’ummar kasar suka kada don fadada ikon shugaba Recep Tayyip Erdogan, yayin da kasashen duniya suka nuna damuwa kan yadda aka kidaya kuri’un zaben.

Shugaban kasar Turkiya, Recep Tayyib Erdogan
Shugaban kasar Turkiya, Recep Tayyib Erdogan REUTERS/Murad Sezer
Talla

A yayin da rikicn siyasa ke neman sake tsananta a Turkiya, shugabar gwamntin Jamus Angela Merkel ta bukaci a tattaunawa tsakanin yan adawa da gawamnati don kwantar da abin da zai biyo baya.

Ana kallon wannan zaben da muhimmanci wajen kawo sauyi a tsarin siyasar Turkiya da ta kasance mamba a kungiyar tsaro ta NATO tun shekarar 1952, sannan kuma take ci gaba da neman kujerar a kungiyar kasashen Turai.

Masu goyon bayan fadada ikon Erdogan sun samu kashi 51.41 yayin da ‘yan adawa suka samu kashi 48.59 cikin 100.

‘Yan adawar sun koka kan sakamakon da suka yi zargin an tafka magudi wajen fitar da shi, lamarin da ya sa suka lashi takobin kalubalantarsa.

A bangare guda, shugaban Faransa Francois Hollande ya ce, zaben raba gardamar don bai wa shugaba Erdogan karfin maido da hukuncin kisa ya saba wa ka’idojin kasashen Turai da Turkiya ke fatan shiga.

Kasar Saudiya da ta kasance aminiyar Turkiya ta yaba da nasarar da shugaba Erdogan ya samu da za ta kara masa karfin iko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.