Isa ga babban shafi
Philippines-Amurka

Ba lallai na amsa gayyatar Trump ba- Duterte

Shugaban Kasar Philippines Rodrigo Duterte ya ce mai yiwuwa ya ki amsa gayyatar Donald Trump na zuwa Amurka dan ganawa da shi.

Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte
Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte REUTERS/Erik De Castro
Talla

Duterte wanda ya karfafa dangantakarsa da tsakanin Philippines da China da Rasha, ya ce ba zai mika kai bori ya hau ba ga kasar ta Amurka.

Sai dai shugaban ya ce huldar diflomasiya tsakanin kasar sa da Amurka ta inganta bayan tafiyar shugaba Barack Obama.

Tsohon shugaban na Amurka ya yi mummunar suka kan yadda Duterte ke kashe mutane baji ba gani da sunan yaki da masu safarar miyagun kwayoyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.