Faransa- Chadi- Sudan
An kubutar da wani Bafaranshe da aka sace a Chadi
Wani Bafaranshe mai aikin hakar ma'adinai da aka sace daga kasar Chadi aka tafi kasar Sudan ya sami kubuta bayan ya shafe makonni shida a hannun wadanda suka yi garkuwa da shi.
Wallafawa ranar:
Talla
Sanarwa daga fadar Shugaban kasar Faransa na tabbatar da sakin Bafaranshen da nuna farin cikin samun shi da rai.
Jami’an tsaron kasar Sudan suka kaddamar da farautar Bafaranshen a watan uku bayan da Ministan kasar Chadi ya sanar da cewa an kai Bafaranshen kasar Sudan.
Bayanai na cewa an sace Bafaranshen ne a kusa da garin Goz Beida dake kudu-maso-gabashin kasar Chadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu