rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Hassan Rouhani

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaban Iran na fuskantar bore daga iyalan masu hakar ma'adinai da suka mutu

media
Shugaban Iran Hassan Rouhani. ®REUTERS/Faisal Mahmood/File Photo

Shugaba Hassan Rouhani na kasar Iran na fuskantar bore daga dangi da ‘yan uwan  mamata masu hakar ma’adinai tara da suka mutu a hadarin da ya lakume rayukan mahakan ma’adinai masu yawa da suka mutu.

 


Shugaba Rouhani na kan hanyarsa ta zuwa inda tsautsayin ya auku ne a wani lokaci da ya rage makonni biyu a yi babban zaben kasar.

Mutane 26 suka gamu da ajalinsu ranar Laraba a lokacin da ramin hakar ma’adinai ya rushe da mutane a ciki.

Ministan Kodago na kasar da kansa ya shiga ramin da ake tono mutanen akokarin da aka yi don ganin ko akwai sauran masu numfashi