Isa ga babban shafi
Afghanistan-Amurka

An kashe Kwamandan IS a Afghanistan

An kashe wani babban kwamandan mayakan IS da ke jagorantar hare-haren ta’addanci a Afghanistan, da suka hada da munmunan harin da aka taba kai wa asibiti in da mutane akalla 50 suka mutu. Hukumomin Amurka da Afghnistan ne suka tabbatar da kashe kwamandan a wani farmakin da dakarun kasashen biyu suka kai a lardin Nangarhar. 

Dakaru na musamman sun kashe Kwamandan mayakan IS a Afghanistan
Dakaru na musamman sun kashe Kwamandan mayakan IS a Afghanistan REUTERS/Omar Sobhani
Talla

Wata sanarwar da fadar shugaban Afghanistan ta fitar, ta ce  dakaru na musamman ne  suka kashe babban kwamandan  da ake kira Abdul Hasib a wani farmakin da suka kaddamar a gabashin lardin Nangerher.

Hasib shi ne kwamandan IS na biyu da dakarun Afghanistan da Amurka suka kashe a cikin watanni 9.

Kisan kwamandan na IS na zuwa ne kwanaki kalilan bayan Amurka ta kai hari da wani katon bom a mabuyar mayakan na IS.

An bayyana Abu Nasib a matsayin wanda ke jagorantar hare-haren IS a Afghanistan, da suka hada da harin da aka kai a birnin Kabul a watan Maris da ya kashe mutane akalla 50.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.