Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka na nazarin tura sojoji dubu 3 zuwa Afghanistan

Kafofin yada labaran Amurka sun rawaito cewa, gwamnatin kasar na nazarin yiwuwar aikawa da sojoji akalla dubu 3 zuwa Afghanistan don yaki da mayakin Taliban.

Akwai kwararrun sojojin Amurka da ke taimaka wa takwarorinsu na Afghanistan a yaki da Taliban
Akwai kwararrun sojojin Amurka da ke taimaka wa takwarorinsu na Afghanistan a yaki da Taliban REUTERS/Anil Usyan
Talla

A karkashin wannan shirin, shugabannin sojin Amurka za su sake samun ikon kaddamar da hare-haren sama kan jagororin Taliban.

Kawo yanzu, shugaba Donald Trump bai rattaba hannu ba kan shirin kamar yadda wata majiya ta bayyana.

Akwai kuma yiwuwar shirin ya bukaci kasashen NATO da su tura dakaru dubu 3 da 500 duk da cewa a halin yanzu akwai sojojin NATO dubu 13 da ke kasar ta Afghanistan, kuma dubu 8 da 400 daga cikinsu na Amurka ne.

A cikin shekarar 2014 ne Amurka ta kawo karshen aikin kakkabe mayakan Taliban a hukumance, amma duk da haka wasu kwararrun sojin kasar sun ci gaba da agaza wa dakarun kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.