rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iraqi Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

kusan mutane 400,000 ne suka tsere daga Mosul

media
Garin Mosul na kasar Iraqi REUTERS/Zohra Bensemra

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane 400,00 suka tsere daga yankunan da mayakan IS suka kwace a kasar Iraqi a tsawon watanni biyu da aka shafe sojojin kasar na kokarin kwato yankin Mosul.


Ofishin kula da ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce akalla mutane 434,775 ne suka fice daga yankunan da ke karkashin ikon kungiyar ta ISIL, sakamakon fadan da ake gwabzawa tsakanin dakarun iraki da mayakan masu da’awar jihadi da suka bazu a cikin tsohon birnin Mosul mai tarihi,

Tun cikin watan fabrairu da ya gabata dakarun Iraqi suka kaddamar da yakin kwato Mosul.

Yawan wadanda suka rabu da matsugunin su Sakamakon wannan yakin na ta karuwa tun a watan oktoban bara, wanda adadin su ya kai dubu 615 da 150 daga lokacin zuwa yanzu.

Ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD ya ce adadin fararen hula dubu talatin ne suka koma gidajen su a yammacin Mosul, tun a karshen watan Afrilu. Wanda hakan ke nuna adadin wadanda suka fice yankin sun haura dubu dari hudu.

Yanzu haka Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta sanar da bude wani sabon sansanin ‘yan gudun hijiran da yakin Mosul ya raba da gidajensu.

An bude sabon sansanin ne a Hasansham da zai dauki yawan yan gudun hijira 9,000.