Ana sa ran Amurka da Korea ta Arewa su koma teburin tattaunawa
Kafafen yada labarai na kasar Korea ta Arewa sun bayyana cewa nan bada dadewa ba, kasar da kuma Amurka zasu tattauna don kawo karshen tsamin da dangantakarsu ta yi.Choe Son Hui babbar darakatar ma’aikatar harkokin wajen Korea ta Arewa ce ta bayyana haka, yayin wata ganawa da ta yi da manema labarai a birnin Beijing na kasar China.
Wallafawa ranar:
Bayanin Son Hui ya zo ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya ce a shirye yake ya tattauna da shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong Un domin tattaunawa kan yadda za’a kawo karshen zaman doya da man ja tsakani Korea ta Arewa da wasu kasashen Duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu