Isa ga babban shafi
Faransa

An yi bikin rantsar da sabon shugaban Faransa Emmanuel Macron

Yau Lahadi sabon shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya karbi rantsuwar fara aiki a fadar Shugaban kasa na Elysee dake Paris, ina zai karbi mulkin daga hannun Francois Hollande.

Fadar shugaban Faransa dake Elysee Paris
Fadar shugaban Faransa dake Elysee Paris REUTERS/Patick Kovarik/Pool
Talla

Emmanuel Macron  mai shekaru 39 ya kasance shugaba mafi kankantar shekaru da ya yi nasarar hawa kujerar shugabancin Faransa.

Emmanuel Macron ya halarci bikin saba rantsuwar ne tare da matarsa Brigitte, amma kuma kasancewa tsohon shugaban Faransa Francois Hollande bashi da mata an yi tsarin yadda za su zauna a wajen bukin rantsuwar.

Bisa dadaddiyar al’adar Faransa ana sa ran bayan rantsuwar, Emmanuel Macron ya kai ziyara ta farko zuwa birnin Berlin gobe Litinin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.