Isa ga babban shafi
China-Africa

Kasar China ta Ware kashe Kudin Amurka Dala Biliyan 124 don Inganta Rayuwa a Duniya

Shugaban China Xi Jinping na karban bakuncin shugabannin kasahe akalla 29 yau Lahadi dake halartan wani taro na kwanaki biyu da niyyar bunkasa tattalin arziki da cinikayya.

Shugaban China Xi Jinping
Shugaban China Xi Jinping RFI
Talla

A jawabinsa wajen bude taron Shugaba Xi Jinping ya alkawarta bada kudin Amurka Dala Biliyan 124 domin inganta rayuwar jamaa aduniya.

A shekara ta 2013 ne kasar China ta kaddamar da wannan shiri na bunkasa harkan ciniki da tattalin arziki da kasashe Africa, Asia da Turai wajen inganta tashoshin jiragen ruwa, layukan dogo, hanyoyin mota da masana’antu.

Tsarin zai shafi kasashen duniya 65 dake nuna kashi 60% na al’ummar duniya, kuma Bankin Bunkasa Kasar China ya ware kudin da ya kai kudin Amurka Dolla biliyan 890 domin ayyuka daban-daban guda 900 da za’ayi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.