rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Vatican Donald Trump

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Paparoma ya ce ba zai yi katsalandan ba gameda batun Bakin haure da Trump ke dauka

media
Paparoma Francis yayin ziyara da ya kai Portugal REUTERS

Paparoma Francis ya ce ba zai tursasawa Shugaban Amurka Donald Trump ya sauya matsayinsa ba dangane da batun bakin haure, da batun Muhalli, a ganawar da za su yi cikin wannan wata.


Paparoma Francis ya fadawa manema labarai jiya kafin ya bar kasar Portugal zuwa gida bayan rangadi na yini biyu da ya kai.

A cewar Paparoma ba zai yanke shawara ba idan yaji bayanai ba tare da ya ji ta bakin kowane bangare ba.

Yanzu haka dai ana ta shaci fadi a kafofin yada labarai na duniya, gameda irin tattaunawar da Paparona Francis da Shugaban Amurka Donald Trump za su yi a ganawan da za su yi ranar 24 ga wannan wata da muke ciki.