Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Dr Sagir Muhammad: Matakan da kariya kan kutsen satar bayanai a Intanet

Wallafawa ranar:

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya ce kasar bata da hannu cikin gagarumin kutsen bayana sirri da manhanja mai illa kan Komfutocin na manyan ma’aikatu, asbitoci da kamfanoni, sama da dubu 200 da aka yi a kasashe 150. Putin ya dora alhakin kai harin da ya fara aukuwa tun a ranar Juma’ar da ta gabata, kan kasar Amurka, wadda ya ce kwararrunta ne suka kirkiro manhajar mai dauke da illa.Kutsen mamaye muhimman bayanan da ke shafin Intanet ko na’ura mai kwakwalwa, shi ne mafi girma da aka taba gani a Duniya, wanda yafi shafar kasashen Birtaniya da Rasha. Kan haka ne Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dr Sagir Muhammad, shugaban wata cibiyar koyar da fasahar mahajojin na’ura mai kwakwalwa da ke jihar Kano a Najeriya, ya kuma yi mana Karin bayani kan yadda al’amarin yake da kuma matakan kariya.  

Kwararru a nahiyar turai sun dukufa wajen magance sake aukuwar kutsen satar bayanan sirri ta kafar Intanet ko na'ura mai kwakwalwa.
Kwararru a nahiyar turai sun dukufa wajen magance sake aukuwar kutsen satar bayanan sirri ta kafar Intanet ko na'ura mai kwakwalwa. REUTERS/Kacper Pempel/Illustration
Sauran kashi-kashi
  • 03:16
  • 03:19
  • 03:26
  • 03:17
  • 03:40
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.