rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Lafiya Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hadarin kamuwa da cutar zuciya daga masu fama da cutar mura da sanyi

media
jami'an kiwon lafiya a wani asibiti dake Turai

Wani binciken masana kiwon lafiya ya nuna cewar an samu karuwar hadarin kamuwa da cutar zuciya daga masu fama da cutar mura da sanyi .
Wannan sakamakon ya tabbatar da wani binciken da aka gudanar a baya dake danganta cutar dake da nasaba da numfashi da kuma wadda ke shafar zuciya.
 


Farfesa Geoffrey Tofler na Jami’ar Sydney da ya jagoranci binciken ya ce tabbas cutar dake da nasaba da numfashi na iya haifar da cutar bugun zuciya.
Sakamakon binciken da aka wallafa a Mujallar kula da lafiya ta ce an gudanar da binciken ne kan mutane 578 da suka kamu da cutar bugun zuciya sakamakon toshewar hanyar jinni.