rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Diflomasiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hassan Rouhani ya sake lashe zaben kasar

media
Hassan Rouhani Shugaban kasar Iran wanda ya sake lashe zaben kasar President.ir/Handout via REUTERS/File Photo

Shugaba Hassan Rouhani na Iran ya sake lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar jiya Juma’a da kashi 57 cikin 100 na yawan kuri’un da mutane fiye da miliyan 40 suka kada.

Yawan kuri’un da ya samu ba sai an sake shiga zagaye na biyu na zaben ba ganin cewa babban abokin hamayarsa mai tsausauran ra’ayi Ebrahim Raisi ya samu kashi 39 cikin dari.
 


Rouhani mai matsakaicin ra’ayi ya ce al’ummar Iran sun samu nasara kuma zai yi bakin kokarin sa tsawon shekaru hudu nan gaba wajen cika ma su alkawurran da ya dauka.

Dama dai Rouhani ya kulla yarjejeniya da kasashe masu karfi fada aji a duniya game da shirin kasar na nukiliya wanda hakan zai bashi damar kawo sauye sauye a kasar.