Isa ga babban shafi
Amurka

Anya Trump na iya sasanta rikicin Isra'ila da Falasdinawa?

Shugaban Amurka Donald Trump ya kai ziyara birnin Kudus da nufin samar da hanyoyin wanzar da zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falasdinawa. Sasanta rikicin Isra’ila da Faladinu dai ya gagari shugabannin Amurka na baya, amma Trump ya ce abu ne mai sauki fiye da yadda mutane suke tsammani.

Shugaban Amurka Donald Trump da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Shugaban Amurka Donald Trump da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu REUTERS/Jona
Talla

A gobe Talata shugaban zai nufi yankunan Falasdinawa domin ganawa da shugaba Mahmud Abbas.

Trump ya gana da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu kuma a cikin jawabinsa ya ce yanzu dama ce ta kawo zaman lafiya a gabas ta tsakiya ta hanyar sake bude kofar tattaunawa tsakanin Isra’ila da Falasinawa.

Sai dai kuma Trump ya jaddada hulda mai karfi da ke tsakanin Amurka da Isra’ila wacce ya kira aminci ne mai karfi da ba mai iya karyawa.

A cewarsa yanzu dama ce ta tabbatar da tsaro da zaman lafiya ga mutanen Isra’ila ta hanyar yakar ta’addanci da makoma mai kyau.

Trump dai ya kasance shugaban Amurka na farko ya kai ziyara babban wajen ibadar Yahudawa inda ya dafa hannayensa a katangar yahudawan kamar yadda suke ibada.

A yakin neman zabensa Trump ya sha alwashin dauke hedikwatar Isra’ila zuwa birnin Kudus matakin da wasu ke ganin shugaban na Amurka na goyon bayan mamayar da Isra’ila ke yi wa Yankunan Falasdinawa.

Masharhanta na ganin Trump surutu ne kawai ya ke domin babu wani cikakken tsari da ya tanadar na sasanta rikicin Isra'ila da Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.