rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Lafiya Habasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An zabi sabon shugaban hukumar kula da lafiya WHO

media
Tedros Adhanom sabon shugaban hukumar kula da lafiya da Duniya WHO. AFP PHOTO/JOSHUA LOTT

An zabi Tedros Adhanom na kasar Habasha a matsayin sabon shugaban hukumar lafiya ta duniya, WHO.

 


Tedros wanda tsohon ministan lafiya ne a Habasha ya doke David Nabarro na Britaniya da Sania Nishtar ta Pakistan da sukayi takarar tare.

A wata sanarwa da ta fitar, Hukumar lafiya ta WHO ta tabbatar da Tedros a matsayin wanda ya yi nasara bayan zagaye na 3 na zaben da aka gudanar.

Tedros mai shekaru 52, kwarare a fanin kula da ciwon zazaben cizon sauro, ya kuma maye gurbin Magret Chan ta Hong Kong, wadda shugabancinta ya gamu da suka kan yadda a baya ta tunkari cutar Ebola a yammcin Afrika.

A jawabinsa na karshe kafin kada kuri’a Tedros ya lashi takobin bijiro da sabbin tsare-tsare da zai inganta sha’ani kiwon lafiya, wanda ake ganin hukumar ta gaza a kansu.

Akwai kuma batun tsarin kiwon lafiya na bai-daya da ya yi alkawarin samarwa, musamman a yankunan da talauci ya fi tsanani, musamman a kasashe masu tasowa.

Tedros ya kara da cewa, ba zai amince mutane su ke mutuwa saboda dalilai na talauci ba.