rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Rasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ana zargin Sirikin Trump da alaka da Rasha

media
Ana zargin Jared Kushner kan badakalar alakar Amurka da Rasha Reuters

Binciken da ake kan rawar da Rasha ta taka a zaben shugabanci Amurka na sake daukan sabon salo, inda sabbin rahotanni da aka bankado ke cewa sirikin shugaba Donald Trump na Amurka ya bukaci tattaunawar sirri da Moscow.


Batun da ke zuwa a dai-dai lokaci da Mista Trump ke komawa kasar bayan rangadi da ya kai wasu kasashen duniya.

A cewar Rahaton idan aka tabbatar da gaskiyar cewa, Jared Kushner, da ke auran babban 'yar Trump, Ivanka, ya kulla alaka da Rasha, to zai sake tabbatar da zargin da ake wa Gwamnatin Trump na fadar Kremlin.