Isa ga babban shafi
Panama

Noriega na Panama ya rasu yana da shekaru 83

Tsohon shugaban mulkin soji a Panama, Janar Manuel Antonio Noriega ya rasu yana mai shekaru 83 da haihuwa kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar a wanna Talata.

Manuel Antonio Noriega na Panama ya rasu yana da shekaru 83
Manuel Antonio Noriega na Panama ya rasu yana da shekaru 83 AFP
Talla

A ‘yan kwanakin nan ne aka yi wa Janar Noriega tiyata sakamakon fama da larurar tsiyayar jini tun bayan da aka yi masa aiki a kwakwaluwarsa.

A lokacin mulkinsa dai, Noriega ya dasa da Amurka kafin a yi amfani da karfi wajen cire shi daga karagar mulki bayan dakarun Amurka sun shiga Panama a shekarar 1989.

Kazalika an kulle marigayin a gidan yarin Amurka bisa zargin sa da ta’ammuli da kwayoyi da kuma wawure dukiyar takakawa.

A cikin watan Janairu ne aka saki tsohon shugaban tare da yi ma sa daurin talala saboda larurar rashin lafiya da ya yi fama da ita.

Tuni shugaba Juan Carlos Varela ya bayyana mutuwarsa a matsayin gagarumin rashi tarihin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.