rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Canjin Yanayi Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Guterres da Narendra sun yi kira a kan kare muhalli

media
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres REUTERS/Tiksa Negeri

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci kasashen duniya da su tashi tsaye domin kare muhallin su wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla a Paris, a dai-dai lokacin da Amurka ke nazarin janyewa daga cikin ta.


Yayin da ya ke jawabin sa na farko kan batun, tun bayan kama aiki, Guterres ya ce ya na da matukar muhimmanci duniya ta aiwatar da wannan yarjejeniya da aka kulla a shekarar 2015.

Kasar Amurka na daga cikin kasashe 147 na duniya da suka kulla yarjejeniyar, amma sabon shugaban na Amurak Donald Trump ya bayyana damuwar sa akan ta, inda yake cewa za ta yiwa tattalin arzikin kasar illa.

Shima Friministan India Narendra Modi ya bayyana cewar rashin sanya hannu ko aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayin da aka kulla a Paris wani babban laifi ne.

Modi wanda ke ziyarar Jamus, ya bayyana aniyar sa kare muhalli saboda mutanen da zasu zo nan gaba, inda yake cewar ya zama wajibi shuagbanin kasashen duniya su tashi tsaye akai.

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta soki shugaba Donald Trump na Amurka saboda kin sanya hannu akan yarjejeniyar kare muhallin.

India ce kasar da tafi cinikayya da Jamus a cikin kasashen da ke cikin kungiyar Turai.