Isa ga babban shafi
Amurka

Sauyin yanayi: Trump zai bayyana matsayar Amurka

A wannan larabar ake saran shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana shirin kasar na janyewa daga yarjejeniyar magance matsalar sauyin yanayin da aka kulla a Paris da ya kunshi kasashen duniya 195.

Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaba Donald Trump na Amurka REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

A sakon da ya aike ta kafar twitter, shugaban ya ce da misalin karfe 3 na rana agogon Amurka zai bayyana matsayin sa a Fadar Shugaban.

Shugaba ya dade yana sukar yarjejeniyar wanda ya bayyana ta a matsayin wadda za ta yiwa tattalin arzikin Amurka illa.

Shugabanni Kasashen Duniya na ci gaba da tir da manufar Trump na yunkurin watsi da yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.