Isa ga babban shafi
Amurka

Putin ya goyi bayan Trump kan canjin yanayi

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce ba zai iya kalubalantar matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka ba na yin watsi da yarjejeniyar Paris ta canjin yanayi.

Vladimir Putin shugaban Rasha
Vladimir Putin shugaban Rasha REUTERS
Talla

Putin da ke jawabi a taron tattalin arziki a Rasha ya yi kira ga kasashen duniya su yi aiki tare da Donald Trump kan sauyin yanayi.

A cewarsa, yanzu abin da ya dace a samar da yanayin da za a tafi tare, amma ba a dinga yin surutu ba, bayan Trump ya ce zai amince a sake tattaunawa domin amincewa da wata yarjejeniyar.

Kasashen duniya dai sun yi tir da matakin da shugaban Amurka ya dauka na janye kasar daga yarjejeniyar rage dumamar yanayi da aka cimma a wata Disamban shekarar 2015 a birnin Paris.

Trump ya ce ya dauki wannan mataki ne lura da irin illolin da yarjejeniyar za ta haifar wa tattalin arzikin Amurka, yayin da ake ganin cewa matakin babban koma-baya ne.

Kasar Amurka ce ta biyu a cikin kasashen da masana’ntunsu ke fitar da gurbataccen iska da ke dumama yanayi.

Martanin kasashen duniya

China kasa ta farko da ke fitar da tururi mai gurbata yanayi a duniya, ta ce duk da wannan mataki da shugaba Trump ya dauka, za ta ci gaba da yin aiki tukuru domin kare yarjejeniyar ta birnin Paris.

Kasashen Jamus da Faransa da kuma Italiya sun yi tir da matakin na shugaban Amurka, tare da yin gargadin cewa ba za su amince a sake bitar yarjejeniyar ba.

Antonio Guttares babban magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana matakin da cewa abin assha ne.

Jean-Claude Juncker, shugaban hukumar kungiyar Tarayyar ya bayyana matakin na Trump a matsayin babban kuskure, tare da cewa yankin Turai zai ci gaba da kare yarjejeniyar.

Firaministar Birtaniya Theresa May, duk da cewa ba ta yi suka ga matakin ba, amma ta ce tabbatar da yarjejeniyar abu ne da ke da amfani ga makomar duniya.

Kasashen kudancin Amurka irinsu Brazil, Argentina da kuma Mexico sun bayyana damuwarsu da matakin na Donald Trump, yayin da Seyni Nafo, shugaban tawagar tattauna yarjejeniyar amadadin Afrika, ke nadamar matakin da Trump ya dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.