rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Afghanistan Kungiyar Kasashen Larabawa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kashe mutane 7 wajen Jana'izar Mamaci a Kabul na Afghanistan

media
'Yan Sanda na sintiri bayan tashin Bam a Kabul, Afghanistan yau Asabar. REUTERS/Mohammad Ismail

Rahotanni daga Kabul na kasar Afghanistan na cewa mutane bakwai ne suka gamu da ajalinsu sakamakon tashin bam da aka dasa a wajen da ake jana'izar wani mamaci da aka kashe jiya Juma'a  yayinda wasu da dama suka jikkata.


Ganau sun bayyana cewa sau uku bama-bamai na tashi a wajen da ake jana’izar Salim Ezadyar wanda ke daya daga cikin mamata hudu da suka gamu da ajalinsu yayin zanga-zangan nuna kyamar Gwamnati da aka yi jiya Jumaa.

Ma'aikatar harkokin lafiya ta kasar na cewa mutane 119 aka kai su asibiti da munanan raunuka.

Bayanai na cewa harabar makabartan da ake jana'izar mamacin ya kasance jina-jina.