rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Batun ta'addanci ya mamaye yakin neman zabe a Birtaniya

media
Mutane 34 sun mutu a cikin kasa da watanni uku sakamakon hare-haren ta'addanci a Birtaniya REUTERS/Neil Hall

Bayan harin da aka kai tsakiyar birnin London a ranar Asabar, barazanar hare-haren ta’addanci ne yanzu ta mamaye yakin neman zaben Birtaniya a yayin da ya rage kwanaki a gudanar babban zabe a kasar.


Barazanar hare-haren ta haifar da zazafarar muharawa kan matakan yaki da ta’addanci a kasar.

Rayukan mutane 34 suka salwanta a hare-haren ta’addancin da aka kai kasa da watanni uku, cikin har da wanda aka kai ranar Asabar a tsakiyar birnin London, in da mutane 7 suka mutu.

Harin dai ya sa an dakatar da yakin neman zabe na kwana guda, kuma yanzu batun barazanar hare-hare ne ya mamaye yakin neman zaben da za a gudanar 8 ga wata.

Jagoran 'yan adawa Jeremy Cobyn ya bukaci Firamista Theresa May ta yi murabus saboda yadda ‘yan sanda dubu 20 suka rasa aiki a lokacin da take rike da mukamin Ministar cikin gida a zamanin gwamnatin David Cemeron.

Jam’iyyar Labour na ganin yawan ‘yan sanda zai taimaka wajen dakile barazanar da kasar ke fuskanta a yau.

Firaminista May ta kaddamar da wani shirin yaki da ta’addanci, in da ta ce daga yanzu babu hukuncin dauri ga laifukan ta’addanci.