rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Chadi Mali Mauritania Burkina Faso Tarayyar Turai Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

EU za ta bai wa Sahel Euro miliyan 50 don yakar ta'addanci

media
Za a kafa rundunar hadaka don yaki da ta'addanci a yankin sahel AFP/Stephane de Sakutin

Kungiyar Kasashen Turai ta amince ta bai wa kasashen Yankin Sahel Euro miliyan 50 domin kafa rundunar hadin gwiwa da za ta yaki masu tada kayar baya a Yankin.


Shugabar Harkokin Diflomasiyar Kungiyar Federico Mogherini ta bayyana haka a birnin Bamako na Mali, in da ta ke cewa samun zaman lafiya a Yankin Sahel na da matukar muhimmanci ga Afrika da kuma Turai.

Jami’ar ta ce, nan bada dadewa ba za a bada kudin domin kafa rundunar wadda za ta kunshi sojoji dubu 5 daga kasashen Mali da Mauritania da Nijar da Chadi da kuma Burkina Faso.

Sai dai shugabannin na Yankin Sahel da suka gana a birnin Riyadh makwannin da suka shude, na son rubanya adadin rundunar daga dubu 5 zuwa dubu 10 saboda girman yankinsu.