Isa ga babban shafi
India

Za mu ci gaba da mutunta yarjejeniyar Paris- India

Gwamnatin India ta kare matakinta na rattaba hannu kan yarjejeniyar dumamar yanayi da aka cimma a birnin Paris, in da ta ce, ta yi haka ne don kare muhalinta amma ba don samun wata riba ta kudi ba.

Kasashen duniya sama da 190 sun sanya hannu kan yarjejeniyar birnin Paris
Kasashen duniya sama da 190 sun sanya hannu kan yarjejeniyar birnin Paris
Talla

Wannan na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana India da China a matsayin kasashen da za su samu ribar biliyoyin Dala a karkashin yarjejeniyar.

Sai dai Ministar Harkokin Wajen India, Sushma Swaraj ta musanta zargin na Donald Trump tare da fadin cewa, za su ci gaba da mutunta yarjejeniyar ko da kuwa Amurka ta janye kanta daga ciki.

Swaraj ta shaida wa maneman labarai a New Delhi cewa, India ta rattaba hannun ne saboda yadda ta yi amanna da muhimancin kare muhalli kimanin shekaru dubu 5 da suka wuce.

Minitar ta ce, wannan sabanin bai shafi hulkdar kasashen biyu ba.

Shugaba Donald Trump dai ya sha caccakar yarjejeniyar ta Paris saboda a cewarsa ta gaza wajen sanya manufofin Amurka a farko.

Trump ya ce, India ta ki amincewa ta rage fitar da turiri kamar yadda sauran kasashen duniya da suka rattaba hannu suka amince.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.