rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Donald Trump

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Comey ya tabbatar da zargin da ake yi wa Trump

media
Comey ya tabbatar da zargin da ake yiwa Trump 路透社

Tsohon Daraktan Hukumar leken asirin Amurka ta FBI James Comey ya shaidawa kwamitin Majalisar Dattawan kasar cewar shugaba Donald Trump ya bukaci ya dai na gudanar da bincike kan tsohon mai ba shi shawara kan harkokin tsaro Janar Michael Flynn.


Comey ya ce a ranar 14 ga watan Fabarairun da ya gana da shugaba Trump a fadar shugaban kasa, ya shaida masa cewar yana fatar zai bar Flynn ba tare da gudanar da bincike a kan sa ba, domin mutumin kirki ne.

Tsohon Daraktan ya ce ya fahimta karara cewar kalaman Trump na nufi ya yi watsi da duk wani bincike da ya ke gudanarwa kan jami’in ne wanda ake zargi da mu’amala da kasar Rasha.