rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Donald Trump

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gwamnatin Trump ta yi “karya”- Comey

media
Tsohon Shugaban Hukumar bincike ta FBI a Amurka James Comey REUTERS/Jonathan Ernst

Tsohon shugaban hukumar bincike ta FBI da aka tube James Comey ya zargi gwamnatin Donald Trump da yi masa karya tare da bata mutuncin shugabancin FBI da ya jagoranta.


Tsohon shugaban hukumar binciken ta FBI ya yi fallasar ne kan gwamnatin Trump da kuma tattaunawar da suka yi da shugaban na Amurka kan binciken alakar shi da Rasha.

Comey wanda ya gurfana gaban kwamitin Majalisar Dattijan Amurka a yau Alhamis ya ce Trump ya bukaci ya ma sa biyayya tare da dakatar da binciken tsohon mai ba shi shawara kan sha’anin tsaro Mike Flynn.

Tshohon Daraktar na FBI ya shafe a sa’o’I uku yana bayani gaban majalisar dattijan Amurka.

Mista Comey ya ce a tattaunawar da suka yi da Trump bayan rantsar da shi a wajen wata liyafar cin abinci a fadar white House a ranar 27 ga Janairu, Shugaban ya yaba masa a aikinsa.

Amma Comey ya ce dalilan da aka kafa kan tube shi daga mukamin shi sun girgiza shi matuka, a yayin da shi ke jagorantar bincike kan kutsen rasha a zaben shugaban kasa.

“Abinda ya ruda ni shi ne lokacin da na gani a telebijin yadda shugaban ke cewa ya tube ni saboda bincike akan Rasha”.

Lauyan da ke kare shugaba Donald Trump ya musanya kalaman na James Comey wanda sai da ya rantse ya fara bayar da shedar a gaban kwamitin da ke bincike game da zargin Rasha ta taimakawa Trump a zaben shugaban kasa.

Lauyan ya ce shugaba Trump bai taba neman Comey ya ma sa biyayya ba, kuma ya kamata ya fuskanci hukunci kan fallasa tattaunawar da suka yi da shugaban ga wani abokinsa zuwa ga ‘yan jarida.

Mista Comey wanda Trump ya tube a ranar 9 ga Mayu ya ce an tube shi ne don sauya akalar binciken Rasha.