rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Chadi Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Chadi Ta Warware Takaddama Tsakaninta da Kamfanonin Mai na Duniya

media
Shugaban Chadi Idris Derby Itno PIUS UTOMI EKPEI / AFP

Kasar Chadi wadda ke daya daga cikin kasashen da suke jin ta a jika sakamakon faduwar darajar man fetur a kasuwannin duniya ta sanar da cewa ta cimma wata yarjejeniya da wasu kamfanonin mai na waje don warware takaddama dangane da batun kudaden haraji.


Yarjejeniyar wanda aka sanya hannu a ciki tun jiya Juma'a bisa jagorancin kamfanin Esso wani reshen kamfanin ExxonMobil na Amurka an kara wa’adin lasisin hako man fetur a yankin Doba har zuwa shekara ta 2050.

Ministan man fetur na kasar Chadi Bechir Madet ya shaidawa kamfanin Dillancin labaran Faransa, AFP cewa akwai kuma yarjejeniyar inganta harkan hako man da ake yi a kasar Chadi.

A watan Oktoba ne wata kotu a Chadi ta ci tara na wasu kamfanonin dake hako mai a kasar saboda haraji na kudade da suka kai kudin Turai Euro Bliyan 67 kwatankwancin kudin Amurka Dolla Biliyan 75.