Isa ga babban shafi
Jamus-Afrika

Kasashen Afrika na taro a Jamus

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel na ganawa da shugabannin Afrika a taron gungun kasashen G20 masu kafin tatalin arziki da aka shirya don tattauna kan yaki da talauci da kuma kwararar ‘yan gudun hijira zuwa nahiyar Turai.

Shugabannin kasashen Afrika tare da Gwamnatin Jamus ,Angela Merkel a birnin Berlin
Shugabannin kasashen Afrika tare da Gwamnatin Jamus ,Angela Merkel a birnin Berlin John MACDOUGALL / AFP
Talla

Makasudin taron na gungun kasashen G20 masu karfin karfin tattalin arziki da ke gudana a birnin Berlin, shi ne hada kan kasashen Afrika da ke fatan kawo sauyi ta hanyar samar da ayyukan yi a nahiyarsu mai fama da barazar tsaro da cin hanci da rashawa, abin da ke jefa tsoro a zukatan kamfanonin kasashen ketare.

Ministan Kudin Jamus Wolfgang Schaeuble ya ce, kasashen duniya na da sha’awar habbakar tattalin arzikin Afrika.

Kasashen da shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ke karbar bakwancinsu a taron na kwanaki biyu sun hada da Masar da Ghana da Cote d’Ivoire da Mali da Niger da Rwanda da Senegal da Tunisia.

Kazalika shugabannin bankin duniya da na asususn bada lamuni na duniya, IMF da kuma kungiyar tarayyar Afrika na cikin mahalarta taron na Berlin.

Ana saran Jamus za ta bai wa Afrikan tallafin Euro Miliyan 300.

Mai magana da yawun Uwargida Merkel, Ulrike Demmer ta ce, akwai bukatar habbaka tattalin arzikin Afrika cikin gaggawa don samar da makoma ta gari ga matasa, abin da zai taka rawa wajen sassauta matsalar kwararar ‘yan gudun hijira zuwa Turai.

A bara ne dai, shugaba Merkel ta kai ziyara kasashen Mali da Niger da Habasha, in da ta yi alkawarin bada tallafin Euro miliyan 27 don yaki da matsalar kwararar baki a Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.