rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

G20 Jamus Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Merkel za ta gana da shugabannin Afrika a taron G20

media
Kungiyar kasashe 20 masu karfin tattalin arzikin duniya REUTERS/Kai Pfaffenbach

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta gana da shugabannin kasashen Afirka da dama domin tattauna batutuwan da suka shafi hanyoyin yaki da talauci da kuma rikice-rikicen da ke haddasa kwararar baki zuwa yankin Turai.


Jamus ce dai ke rike da ragamar shugabancin kungiyar kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya G20, inda aka gayyaci shugabannin Masar da Ghana da Cote d’Ivoire da Mali da Nijar da Rwanda da Senegal da kuma Tunisia a taron da za a soma a yau Litinin.

Taron zai shafi tattauna yadda kasashen Afrika za su bude kofa ga kamfanonin kasashen Turai domin saka jari wanda zai taimaka ga samar da ayyukan yi a Nahiyar.

Sannan Jamus za ta tattauna da shugabannin kasashen na Afrika kan matakan rage kwararar mutane zuwa Turai.

Shugabar Jamus Angela Merkel za ta yi amfani da taron domin jaddada alkawalin da ta dauka na ba kasashen Afrika tallafin kudi yuro miliyan 27 domin hana kwararar ‘yan ci-rani zuwa Turai.