rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Biafra

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan Biafra sun nesanta kansu da Nmandi Kanu

media
Nnamdi Kanu mai fafutukar kafa kasar Biafra daga Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde

Shugaban Kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra a MASSOB, Ralph Uwazurike ya nesanta kansa da Nnamdi Kanu da ke neman amfani da tashin hankali a fafutukarsa.


Yayin ganawa da wasu shugabanin kungiyar arewa a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya domin ganin an fahmci juna, Uwazurike ya bukaci samar da zaman lafiya tare da yin bayani kan yadda kungiyar MASSOB a karkahinsa ta kwahse shekaru 18 tana fafutuka ba tare da yamutsi ba.

Uwazurike ya yi bayani kan yadda ya kafa Radio Biafra, in da ya sanya Nnamdi Kanu a matsayin darekta a tashar, amma 'yan siyasa suka yi amfani da shi wajen sauya manufar kafa tashar.

Shugaban ya ce, manufar kafa gidan rediyon ita ce, wayar da kan al’ummar Igbo da kuma ilmantar da su, amma aka mayar da rediyon wani dandalin yada sakwannin kyama da makarkashiya da kuma razanar da jama’a.

Uwazurike ya bada tabbacin cewa, babu abin da zai samu 'yan arewa da ke rayuwa a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Wannan dai na zuwa bayan hadakar kungiyar matasan arewa ta bai wa ‘yan kabilar Igbo wa’adin ficewa daga yankin, al’amarin da ya janyo cecekuce a dukkanin fadin kasar.

Kungiyar Dattawan Arewa ta fito daga bisani ta nuna goyon bayanta ga kiran da matasan suka yi.