rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya Muhalli

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gobara ta kashe mutane da dama a London

media
Ginin Grenfell Tower da ya kama da wuta a birnin London REUTERS/Toby Melville

Akalla Mutane 12 aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon wata mummunar gobara da ta tashi cikin dare a wani dogon bene mai hawa 27 a birnin London na Birtaniya.


 

‘Yan sandan Birtaniya sun ce adadin wadanda suka mutu na iya karuwa a yayin da ake ci gaba da aikin kashe gobarar da ceto mutanen da suka makale a benen.

Mutane da dama ne suka jikkata wadanda har zuwa yanzu ba a iya tantance adadinsu ba, kodayake hukumomin lafiya sun ce mutane kusan 50 ke kwance a gadon asibiti.

 

Rundunar ‘yan sandan London ta tabbatar da mutuwar mutane 12 a gobarar da ta ci dogon benen mai hawa 24.

Kwamandan ‘yan sandan a London Stuart Cundy ya ce adadin zai karu a yayin da ake ci gaba da aikin agaji da zai dauki kwanaki.

Rahotanni sun ce, akalla jami'an kwana-kwana 200 ne ke aikin kashe gobarar, tare da ceto mutanen da suka makale a ginin na Grenfell Tower.

Jami’an kashe gobara sun danganta al’amarin a matsayin mafi girma

Jami’an kiwon lafiya sun ce, a halin yanzu, akwai fiye da mutane 50 da ke samun kulawa a asibiti.

Ana fargabar cewa, ginin na Grenfell Tower zai ruguje saboda yadda wuta ta yi ma sa mummunan lahani.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani game da musabbabin tashin gobarar da ta fara tun a tsakiyar dare.