rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

UNICEF Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

1 cikin yara 5 a kasashen da suka samu ci gaba na cikin Talauci

media
Cikin ko wadanne yara 5 a kasashen duniya da suka ci gaba, yaro guda na fama da talauci. DR

Wani Rahotan hukumar UNICEF da ke kula da kananan yara ya ce cikin ko wadanne yara 5 a kasashen duniya da suka ci gaba, yaro guda na fama da talauci, kuma matsalar tafi girma a Amurka da New Zealand.


Alkaluman hukumar ya ce kusan kashi 13 na yawan yaran wadanan kasashe da suka ci gaba basa iya samun abinci mai gina jiki, yayin da kididigar ya kai kashi 20 a Amurka da Burtaniya.

Sarak Cook, Daraktar hukumar ta ce samun albashi ko kuma kudin shiga mai yawa ba wai shine ke inganta rayuwar yara ba, kuma hakan na iya haifar da ban-banci.

Rahotan ya duba batutuwa da dama da suka hada da samun ilimi, kula da lafiya, shan giyar da ta wuce kima da tattalin arziki da kuma muhalli.