rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Morocco Emmanuel Macron Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Macron ya kai ziyara Moroko don tattauna yaki da ta'addanci

media
Shugaban Faransa Emmanuel Macron a fadar Rabat da ke Moroko REUTERS/Alain Jocard/Pool

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, yanzu haka yana ziyarar kasar Moroko inda zai tattauna da hukumomin kasar kan yaki da ta’addanci da kuma rikicin kasashen Libya da Qatar.


Kasar Moroko na daga cikin kasashen da ke marawa Qatar baya a rikicin da ta ke da Saudiya, kana kuma ana ganin tana da rawar da zata taka wajen magance rikicin kasar Libya.

Fadar shugaban Faransa ta ce, kafin isar shugaba Macron sai da ya tattauna ta waya da shugabanin kasashen Afirka ta Arewa.

A lokacin zantawa da Manema labarai, Mista Macron ya ce Faransa da Moroko a shirye suke don gani sun shiga tsakani don samar da sulhu da mayar da huldar diflomasiya tsakanin kasashen na yankin tekun fasha.

Macron ya ce akwai bukatar dawo da zaman lafiya tsakanin kasashe, wanda ko ba komai, suna da ruwa da tsaki a rikicin kasashen Syria da Libya.