Rasha ta ce mai yiyuwa ne ta kashe al-Baghdadi
Rasha ta ce tana tunanin dakarunta sun kashe jagoran kungiyar IS Abu Bakr al Baghdadi da ke da’awar jihadi a Syria da Iraqi a wani hari da suka kai a Raqqa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rundunar sojin Rasha ta ce tana bincike domin tabbatar da yiyuwar mutuwar jagoran kungiyar ‘yan ta’addan da ake kira Daesh.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Rundunar sojin Rasha ta ce akwai yiyuwar al-Baghdadi na daga cikin mutanen da aka kashe a wani hari da aka kai kusa da Raqqa na Syria a ranar 28 ga watan mayun da ya gabata.
Sanarwa tace an kai harin ne a lokacin da shugaban na IS ya tara mayakansa yana tsara dubarun ficewa daga yankin na Raqqa da ake wa luguden wuta ta sama.
Sanarwar ta kara da cewa manyan kwamandojin IS kusan 30 da mayakan kungiyar 300 aka kashe.
Sai dai rundunar ta Rasha ta ce tana ci gaba da tattara bayanai domin tabbatar da hakikanin gaskiyar abin da ya faru.
Amurka ta ce ba za ta yi gaggawar tabbatar da rahoton mutuwar Baghdadi ba.
Idan har labarin ya tabbata, hakan zai kasance babbar nasara ga Rasha wadda ta kaddamar da yaki da ayyukan ta’addancin IS musamman a Syria.
A cikin dare ne aka kai harin ta sama, kuma cikin wadanda aka kashe har da Sarkin Ragga da babban jami’in tsaron IS, a cewar Rasha.
An dade dai ana ikirarin kisan Baghdadi, ko raunata shi, wanda hakan ya sa ake wa jagoran na IS kirari da sunan fatalwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu