rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Syria Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Za'a Sake Zaman Tattauna Rikicin Syria a Geneva Ranar 10 ga Watan Gobe

media
Jakadan Majalisar Dinkin Duniya Staffan de Mistura REUTERS/Pierre Albouy/File Photo

Tattaunawar sulhu gameda yakin da ake yi a kasar Syria, wanda Majalisar Dinkin Duniya ke daukan nauyin  shiryawa  zai gudana ne ranar 10 ga watan gobe a Geneva.


Jakadan Majalisar Staffan de Mistura ya sanar da haka yau inda yake cewa za’a ci gaba da tattaunawan ne a cikin watan Augusta da Satumba na wannan shekara.

Ranar 19 ga watan jiya aka yi tattaunawan sulhu na karshe.

Su dai ‘yan adawa a Syria sun tsaya kai da fata  sai Shugaba Bashar Assad ya sauka kafin dukkan sulhu.

Mutane akalla dubu 320 suka mutu sakamakon wannan yaki da ake yi a Syria tun shekara ta 2011.