rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Qatar Saudiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasar Qatar ta Nemi Sulhu da Kasashen Larabawa

media
Ministan waje na kasar Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman al-Thani Reuters

Kasar Qatar ta roki kasashen Larabawa makwabtan ta da suka janye hulda da ita da su cire mata dukkan wani takunkumi don komawa kujeran tattaunawa da ita.

 


Wannan roko na zuwa ne bayan da kasar Daular Larabawa ke cewa maida Qatar saniyar ware na iya kai shekaru da yawa a haka.

Ministan Waje na kasar Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani ya bayyana cewa jerin takunkumin da aka malkaya masu ya saba hankali.

Ya ce duniya ta sani cewa suna  bukatar zama a yi sulhu amma ba da rana tsaka a malkaya masu takunkumi ba.

A ranar biyar ga wannan wata ne dai Kasar Saudiya da kawayenta, Bahrain, Daular Larabawa da sauransu suka malkayawa Qatar takunkumin karairaya ta saboda zargin tana marawa kungiyoyin ta’addanci baya.