Amurka da China sun tattauna barazanar Koriya ta Arewa
An yi wata tattaunawa tsakanin manyan jami’an gwamnatin Amurka da na China kan barazanar Koriya ta arewa na mallakar makaman nukiliya. Tattaunawar na zuwa bayan shugaba Donald Trump ya bayyana cewa China ta gaza shawo kan gwamnatin Pyongyang game da dakatar da shirinta na mallakar makaman.
Wallafawa ranar:
Sakataren harakokin wajen Amurka Rex Tillerson da na tsaro Jim Mattis ne suka yi tattaunawar da takwarorinsu na China.
Amurka ta ce babbar manufar ganawar ita ce tabbatar wa China bukatar janyo hankalin gwamnatin Kim Jong-Un na ya jingine shirin kasarsa na mallakar makaman nukiliya.
Tun rantsar da Donald Trump ya bayyana cewa dakatar da barazanar nukiliyar Koriya ne babban abin da zai sa gaba a manufofinsa na kasashen ketare, ta hanyar neman taimakon china.
Sai dai kafin soma tattaunawar da aka gudanar a jiya Laraba tsakanin Amurka da China shugaba Trump ya fito a Twitter yana cewa China ta gaza duk da ya yaba da kokarin shugaba Xi Jinping akan Koriya, amma a cewarsa haka ba ta cimma ruwa ba.
Trump dai bai fadi abin da zai iya biyo wa baya ba idan har China ta gaza shawo kan aminiyarta Koriya ta arewa kan bukatar Amurka na dakatar da shirin nukiliya da mallakar makamai masu linzame.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu