Firaminstan India na Ziyara a Amurka
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya karbi bakuncin Firaministan kasar India Narendra Modi a fadar Gwamnati na White House karon farko gaba-da-gaba domin kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.
Wallafawa ranar:
Wannan na zuwa ne duk da bambancin ra'ayi tsakanin manyan kasashen biyu dangane da batun matsayin bakin haure da kuma batun rage dumamar yanayi.
Shugaba Donald Trump ya bayyana Firaministan India a matsayin aboki na kwarai.
Kasar India na matsayin babbar kasa mai hanzarin samun bunkasar tattalin arziki, wanda Firaministan ke kokarin ganin kasar ta dore da wannan mataki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu